(ABNA24.com) Firai ministan na kasar Italiya, Giuseppe Conte ya bayyan ahakan ne a wata tattaunawa ta yawar tarho da ya yi da shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani, ya kuma tabo batun fada a cutar corona, yana mai cewa; mun san yadda ku ke ji, kuma za mu yi maraba da duk wani aiki tare a tsakanin kasashen biyu domin fada da cutar.
Firai ministan na kasar Italiya ya kuma jaddada muhimmancin fadada alaka a tsakanin kasarsa da kuma Iran, musamman a fagen yarjejeniyar Nukiliya da kuma kafar musayar kudi ta ( Instex) da kasashen turai.
Conte ya kuma kara da cewa; wajibi ne a yi aiki da duk wata dama da ake da ita domin tabbatar da zaman lafiya a cikin yankin gabas ta tsakiya.
/129
22 Afirilu 2020 - 05:29
Lambar labari: 1028475
Firai ministan na kasar Italiya, Giuseppe Conte ya bayyan ahakan ne a wata tattaunawa ta yawar tarho da ya yi da shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani, ya kuma tabo batun fada a cutar corona, yana mai cewa; mun san yadda ku ke ji, kuma za mu yi maraba da duk wani aiki tare a tsakanin kasashen biyu domin fada da cutar.